Magoya bayan Manchester City sun yi ta mayar da martani ga wani sako da aka wallafa a Twitter wanda ke nuna wani rahoto da ke cewa Pep Guardiola na tunanin zawarcin Frenkie de Jong bayan yanke shawarar yin watsi da zawarcin Declan Rice na West Ham United.

 Manchester City ta kawo karshen zawarcin dan wasan West Ham Declan Rice bayan da Arsenal ta dawo da tayin fan miliyan 105.

 A baya Manchester United ta nemi De Jong wanda tayi yunkurin kawo dan kasar Holland din zuwa Old Trafford gaba dayansa a kasuwar bazara na bara kafin ya amince da cigaba da zama a Spain.

 Sai dai kuma a wani yanayi na ban mamaki, rahotanni sun nuna cewa Manchester City ta shiga zawarcinsa. United za ta fusata idan abokan hamayyar ta suka doke ta.

 A cewar wani rahoto da jaridar The Sun ta buga, Pep Guardiola na sha’awar siyan dan wasan na Barcelona. Amma rahoton ya ce Barcelona za ta so akalla fan miliyan 90 da ta yi niyyar ba wa West Ham akan Declan Rice.

 Wannan sauye-sauyen dabarun, kamar yadda jaridar Sun ta ruwaito, yana nuna kyakkyawar niyya ta City don nemo wanda zai maye gurbin Ilkay Gundogan wanda kwanan nan ya koma Camp Nou.

 Guardiola ya kasance babban mai son De Jong dan wasan tsakiya, a baya bai yi nasara ba lokacin da ya yi kokarin kulla yarjejeniya shekaru hudu da suka wuce.

 Rahoton da aka yada a shafin Twitter ya tattara amsoshi da dama daga dimbin magoya bayan Man City.

Daga naku har kullum NHK.