Bayan da kamfanin Twitter ya sanar da takaitawa masu amfani da shafin adadin Abinda zasu iya karantawa a cikin yini guda, ‘yan Najeriya da dama sun fara Æ™aura zuwa Truth Social a matsayin madadin Twitter.


Ko da yake Twitter ya soke manufar, hakan bai hana yin hijira zuwa ga Truth Social ba.


An kafa Truth Social ta tsohon Shugaban Amurka Donald Trump bayan dakatar da shi na dindindin daga Twitter, saboda zargin da ake masa na tunzura masu zanga-zangar da suka kai hari a ginin Capitol na Amurka a watan Janairun 2021.


Har lokacin da Twitter ta bada sanarwar takaita adadin Abinda masu amfani da ita za su iya karantawa a cikin yini guda, Truth Social ba ta da farin jini sosai a tsakanin 'yan Najeriya.


Amma bayan masu amfani da Twitter sun fara samun matsala wajen shiga cikin Manhajar saboda takunkumin da aka sanya a dandalin, Truth Social ta shahara.


Truth Social ta yi ba'a ga Twitter tana cewa: "Tunawa: Akan Truth Social za ku iya karantawa,  daura Truths gwargwadon yadda kuke so - duk kyauta."


Daga Naku Har Kullum wato NHK