Daya daga cikin Manyan tawagar Ingila, Chelsea ta yi mamakin irin rashin nasarar da tayi a kakar wasan da ta wuce, yayin da kungiyar ta kare kakar bana ba tare da kofuna ba sannan kuma ta kasa samun tikitin shiga gasar Turai a kakar wasa mai zuwa.

 Yanzu haka dai kungiyar ta Blues ta fara siyar da manyan ‘yan wasanta domin samar da fili ga sabbin ‘yan wasan da ke shigowa da kuma sake gina kungiyar a karkashin sabon koci, Mauricio Pochettino. 
 
Havertz, Mason Mount da Kyaftin Club, Azpilicueta suna cikin manyan taurarin da suka bar kulob din.

 Duk da cewa magoya bayan kungiyar sun fusata kan yadda Chelsea ke siyar da 'yan wasanta, ga wasu dalilan da suka sa Chelsea ta yanke shawarar siyar da wadannan 'yan wasan.

 1. Bayar da Dama ga Sabbin yan Wasa:


 Chelsea tana da 'yan wasa da yawa a kakar wasan da ta gabata, duk da hakan yana da kyau, amma kuma hakan ya haifar da matsala gurin zaben wadanda zasu buga wasa daga Manajan.
 
Ta hanyar rage 'yan wasa daga kulob É—in zai taimaka wajen samar da dama ga sababbin 'yan wasa don shiga cikin tawagar.


 2.Sake gina Squad:


 Chelsea ta dauki Mauricio Pochettino a matsayin sabon kocin kungiyar kuma duk lokacin da sabbin manajoji suka shigo kungiyar za su so su gina kungiyar don dacewa da salon wasansu.
 
’Yan wasan da ke barin kulob din basa cikin shirin sabon Manaja na Chelsea, don haka yana da kyau su bar kungiyar ta yadda za a samu isasshen fili don sake gina kungiyar.


 3. Fitar da Æ´an wasa:


 Yawancin 'yan wasan da Chelsea ta siyar ba su kasance cikin kyakkyawan yanayi a kwanan nan ba. Sun kasance ba su da kyau yayin da wasu suka yi rauni. Hakan na nufin Chelsea na siyar da wadannan 'yan wasan ne domin kawar da 'yan wasan da ba su taka rawar gani a kulob din ba.


 Yanzu dai Chelsea ta siyar da Kai Havertz da Mason Mount da Kovacic da Ngolo Kante da wasu ‘yan wasa. Magoya bayan kungiyar za su yi fatan cewa sayar da wadannan 'yan wasan babbar nasara ce ga kungiyar kuma da kuma fatan samun kyakkyawan yanayi.

 Me kuke tunani?, Shin Chelsea na yanke shawara mai kyau ta hanyar sayar da 'yan wasanta?

Daga Naku Har Kullum NHK.