A jiya 1 ga watan Yuli ne aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara, yayin da kowace kungiya za ta iya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya daga kowane lungu na duniya.
 
 Yawancin kungiyoyi sun shirya yin amfani da wannan damar don gina kungiyarsu kafin a rufe tagar Sayayyar a ranar 30 ga Agusta. 
 
An fara sanya hannu kuma wasu kungiyoyi sun sanar da sabbin ‘yan wasan da aka cimma yarjejeniya.

Ga hudu daga cikinsu:

1. Dominik


Dominik ne zai zama dan wasa na biyu da Liverpool ta dauko daga Leipzig a wannan bazarar. 

 Ana yin gwaje-gwajen likita, kuma an sanya hannu. Sanarwa a hukumance za ta biyo baya a mako mai zuwa da kuma sabon lambar rigarsa ta Liverpool da za a bayyana.


2. Celtic Jota


An tabbatar da cewa tauraron Celtic Jota zai koma Al Ittihad a wannan bazarar kuma sabon kulob din nasa yana shirya takardu don kammala yarjejeniyar a hukumance da kuma jami'in da zai biyo baya.


3. Jurrien Timber


Arsenal ta kusa kammala yarjejeniya tsakaninta da Ajax kan Jurrien Timber, kamar yadda Fabrizio Romano ya fada, yarjejeniyar ta yi kusa kuma za ta kammala a mako mai zuwa.

4. Marcelo Brozovic


A yayin da shi kuma É—an wasa Marcelo Brozovic ya gama gwajin lafiya da Al Nassr.

Daga Naku Har Kullum NHK