WhatsApp ya kasance ɗaya daga cikin Social Media da ya fi shahara a duniya wanda yasa ya zama babban manufa ga masu kutse.

Duk da tsauraran tsaro da yake dashi kamar end-to-end encryption da sauran su.

’Yan damfara na yanar gizo saida suka samo hanyoyin da suke bi gurin shiga Asusun mutane.

Buy Now 👇👇👇

Kuma ba komai yasa suke wannan ba inba kudi ba, kodai ta gurinka ko Abokanan ka ko kuma Iyalan ka.

To Amma ta yaya za ku iya sanin ko an shiga Asusun ku?

A wannan Darasin zamu tattauna akan Wadannan hanyoyin da zaku gane ana bibiyar Asusun ku da kuma yadda zaku kare kanku.

1. WHATSAPP WEB

Abu na farko shine WhatsApp web wanda shine yin Amfani da Asusun WhatsApp akan kwamfufa, wanda anayin Amfani da WhatsApp web domin bibiyar duk Chatting din da Mutum yake yi.

An fiddo WhatsApp web ne domin bada dama ga masu son suyi chatting na WhatsApp a kwamfuta.

Wanda daga baya masu kutse suka maida shi hanyar da suke sace Account ɗin mutane.

Amma abin burgewa shine zaka iya gane mutum nawa ne suke bibiyar Accounts dinka, wanda da Zaran kaga wani abu da baka gane ba zaka iya ɗaukar mataki.

Ma'ana duk wani abu da baka fahimta ba zaka iya daukar mataki domin kariya ga Account dinka.

Yadda zaka gane idan ana bibiyar Account ɗinka na WhatsApp

Zaka iya ganin List na waɗanda suke bibiyar Account ɗinka na WhatsApp, ga yadda zakayi.

KARANTA: Yadda ake Gane Wanda Suka karanta Saqon ka a Group na

Da farko ka buɗe WhatsApp ɗinka

Daga nan saika tafi zuwa Setting a wani WhatsApp ɗin ba cikin Setting yake ba.

Daga nan saika danna Linked Devices

Bayan ka danna Linked Devices Idan kaga ba'a bibiyar ka to ka godewa Allah sai kuma ka qara tsaro.

Anan zakaga duk masu bibiyar ka, Saika zaɓi duk wanda baka gane ba Saika ɗauki mataki nayin Log out.

Anan ne muka kawo qarshen darasin mu na yau da fatan wannan Darasin ya qayatar daku, saboda haka kuyi share zuwa ga'yan uwa da Abokan arziki domin suma su Amfana