Jama'a barkan mu da sake kasancewa daku a wannan sabon darasin a inda zani kawo maku wani website da zakuyi amfani dashi gurin yin kasuwanci na sayar da Data dama Abubuwa da dama Kuma ku sami Riba Sosai.

    Yadda ake Amfani da Data a wannan zamanin

    Sanin kankune cewa amfani da Data ya kasance Abinda kowa keyi, domin duk wanda yake da waya wadda take hawan Internet to dole yana buqatar data koda ko Chatting kawai yake yi. Kuma kai kanka kasan da haka domin idan ka qirga nawa kake kashewa a wata guda gurin sayen Data zakaga cewa kudade ne ba 'yan kadan ba kuma wannan fa Mutum guda kenan to idan ka qirga a unguwar ku zakaga Mutane suna kashe kudade sosai.

    Wannan dalilin yasa na kawo maku wannan website wanda ni kaina ina amfani dashi gurin Sayen Data kaga kenan koda baza kayi Kasuwancin ba zaka iya amfani dashi gurin Sayen Data wadda zaka ringa Amfani da ita kaga ka samu sauqi akan yadda kake saye da, Kuma wannan website É—in kyauta ne yin Register.

    Sunan Website É—in Gladtidingsdata.com

    Gladtidingsdata shine sunan wannan website É—in wanda mutane da yawa suna amfani dashi kuma suna jin dadin shi. Kuma ba iya website kawai garesu ba suna da Application wanda zaka iya yin Downloading dinshi a Playstore kyauta.

    Karanta: Yadda Zakaga WaÉ—anda Suka Karanta Saqon Daka Tura a Group na WhatsApp

    Yadda zaka yi Register a Gladtidingsdata.com

    Yin Register a wannan website É—in yana da Matukar Sauqi kawai ka dana Gladtidingsdata bayan ka danna zaya wuce dakai inda zaka yi Register.


    Da farko Bayan ya kawo ka inda Zaka yi Register zaka Saka:

    • Full name wato sunan ka da sunan Mahaifinka Misali (Nasir Hassan).
    • Username wato sunan da zaka ringa Amfani dashi Misali (Nasir2020)
    • Email address ka tabbatar yana aiki domin zasu tura maka saqo domin kayi verifying din Account É—in ka Misali (misali@gmail.com)
    • Phone number wato Lambar wayar ka Misali (08123456789)
    • Address wato garinku Misali (Abuja)
    • Refferal Username wato Username na wanda Ya gayyace ka ga Abinda zaka saka (Nasirknk02)
    • Password ka tabbatar ka zabi Mai kwari kamar haka ( #Na5177sir) saika maimaita Password din Domin kayi Confirming dinshi.

    Idan kayi gaba daya wannan to kagama Register saika je zuwa Email É—in ka zakaga sun tura maka Saqo wanda zakayi Verifying din Account É—in saika danna Link din.


    Bayan kayi verifying din Account É—in ka saika je kayi Login.

    Yadda ake saka KuÉ—i Domin fara Sayen Data

    Shidai wannan website yana da hanyoyi guda Uku da ake saka Kudi.

    1. Hanya ta farko itace tayin Transfer a inda zasu baka Account number wadda Duk lokacin daka turo kudi ga wannan Account number kaitsaye zasu shiga cikin Wallet din. Amma kasani duk lokacin dakayi amfani da Transfer gurin Turo kudi to zasu dauki Charges na ₦50 kuma ko nawa zaka turo zasu dauki wannan ₦50 kawai.
    2.  Hanya ta Biyu itace Sayen Coupon a inda zakayi Chatting dasu ta WhatsApp a inda zaka sayi na daidai kuÉ—in ka saika zo kayi amfani da Coupon É—in domin ka saka kuÉ—i a cikin Wallet din.
    3.  Hanya ta uku itace tayin amfani da ATM wadda wannan hanyar tana da sauqin Charges idan aka haÉ—a ta da saka kudi ta hanyar Transfer.Wadannan sune hanyoyin da ake saka kuÉ—i cikin wannan Wallet din Domin yin kasuwancin sayar da Data.

    Yadda ake Sayen Data a website din

    Bayan ka saka kudi sai kaje zuwa Buy Data inda zaka zabi Network wato Mtn ko Airtel ya danganta da Network din da kakeso ka sayama datar daga nan Saika Zabi Farashin da kakeso.

    Wasu Abubuwan da Website din ya qunsa Bayan Sayen Data

    Kasani cewa ba iya Data Kawai ake saidawa a Wannan website É—in ba zaka iya sayen Airtime, ko Bill na Tv ko na NEPA ko duba Jarabawa (WAEC, NECO etc.) dama Abubuwa da dama. Saboda haka ku garzaya kuyi Register domin ku fara more wannan Garabasar.

    Bayanin Rufewa

    Wannan shine qarshen darasin mu na yau da fatan ya qayatar daku, duk wanda yake da wata tambaya sai yayi ta a comment, Nagode sai mun hadu a Darasi nagaba.