@ NHKTECH @


Shin Kuna samun kira daga lambobin da baku sani ba, kira nawa kake samu daga private number, Ba kai kaÉ—ai ba ne kake cikin bacin rai ta ga wadannan masu kiran. Shin Kuna son sanin yadda ake gano masu kiranku da Private number. 

Me ake kira da Private Number? 

 Lokacin da mai kira ya boye Lambar shi da gangan ga Wanda yake kira wannan shine ake kira da "Private Number". 

 Yi amfani da Truecaller app domin gano unknown Number 

 Wannan ita ce hanya mafi sauqi don gano lambar sirri da ke kawo cikas gareku. True caller App bai zama boyayye ba ga wasu domin Mutane da Yawa suna amfani dashi, truecaller app zai baka dama a lokacin da aka kira ka da unknown number zakaga cikakken sunan Wanda ya kira ka wani lokaci harda location na Wanda ke kiran ka. 

 Gano unknown number Ta hanyar Amfani DA *30#

Wannan Wata hanyace ta gano wanda ke kiran wayarka. Idan kun gaji da samun kira daga lambobin da baku sani ba kuma ba ku san yadda za ku dakatar da su ba, saiku danna *30# da zarar sun kashe. Ta wannan hanyar, za a aiko muku da SMS tare da lambar wayar su. Zai taimake ka wajen bibiya da tantance wanda ke yin kutse da kuma wargaza kwanciyar hankalinka.

Bayan an Turo Maka Saika kira ko kuma kayi bincike akan ta. 

'Yan uwa wannan Shine qarshen darasin mu na yau DA fatan ya qayatar daku.