@ NHKTECH @
  'Yan uwa Barka da wannan lokaci sannun mu da saduwa acikin Sabon Darasi. A wannan Darasin zani koyar da yadda zakaga wadanda suka Karanta saqon daka Tura a Group na WhatsApp. 

  Nasan mutane da yawa suna so susan waÉ—anda suka Karanta saqon da suka tura a cikin Group na WhatsApp, saboda shi saqon da aka tura a cikin Group na WhatsApp ba É—aya bane da saqon daka turawa Mutum Daya, domin shi saqon daka turawa Wani zaka iya ganewa ya karanta shi ko bai karanta ba.

  SaÉ“anin na Group bazaka iya gane waÉ—anda suka Karanta shiba domin Group ba Mutum Daya bane. To amma ga wasu hanyoyin da zakabi domin kagane waÉ—anda suka Karanta Saqon ka.

Hanyoyin da zakabi Sune:

 Da farko; Zakaje Zuwa WhatsApp Application É—inka saika buÉ—e shi.

  Na Biyu; Bayan ka BuÉ—e shi, Saikaje Zuwa Group É—in daka tura saqon. 

 Na Uku; Bayan ka shiga cikin Group É—in, Sai kaje kaitsaye zuwa saqon daka Tura.

  Na HuÉ—u; Bayan kaje kan Saqon saika Danne shi Har sai yayi Marking. 

 Na Biyar; Bayan yayi Marking Zakaga Dugo Guda Uku can Sama Bangaren Dama, saika danna shi. 

  Na Shida; Bayan ka danna shi Zakaga Jerin Rubutu, daga ciki zakaga an Rubuta "Info" Saika Danna shi. 

 Na Bakwai; Bayan ka danna "Info" Zakaga Jerin wadanda suka Karanta an rubuta masu "Read by". 

Duk waÉ—anda sunansu ya biyo bayan "Read by" sune suka Karanta saqon. 

 Sai kuma zakaga an Rubuta"Delivered to" Ma'ana su Saqon yaje Masu amma basu karanta ba Sai kuma "Remaining" Ma'ana Su basu hau online ba bare yaje Masu. 

 _By NHK

 Idan wannan Darasin ya Qayatar daku to kuyi Like Akanshi, Sannan kuyi comment da Tambayoyi ko Ra'ayin ku, Sannan kuyi Following É—inmu ta Danna alamar Follow Domin Samun Sabbin Darussan mu. 

 Kuma Kada ku Manta Kuyi Like Akan Page É—in mu na Facebook Mai Suna "NHKTECH" Domin Samun Sabbin Abubuwa da Suka Shafi Technology.