'Yan uwa Assalamu Alaikum Sannun mu da sake Kasancewa a wani sabon Darasi. 

A wannan darasi Zani koya yadda zaku dauko (Download) Application a Play Store koda babu shi A qasarku ma'ana koda ba'aba 'yan Qasarku damar dauko (download) shiba. 

Ga Hanyoyin da zakubi

1)Da farko idan Ka samu wannan Matsalar kawai Abinda zakayi shine Agurin da suka rubuta maka haka wato Acikin Playstore din, Ka duba daga Sama Zakaga wasu Dugagga Guda uku Daga sama Hannun dama saika danna shi. 

2)Daga nan Zaka Option guda uku saika zabi na farko wato Share bayan ka danna share zakaga Copy saika danna shi. 

3)Bayan Kayi copy din Kawai  sai kaje zuwa Browser dinka Ko wace kalace Sai kayi Searching din wannan website din "Apkcombo" bayan ya bude zakaga gurin Searching saika kayi Pasting din wannan Link da kayi Copy daga Playstore saikayi Searching. 

4)Daga nan Application din zai Bayyana saika Danna Download. 

5)Daga nan zaya wuce dakai daga nan zakaga Ya nuno Application din tare da da wasu bayanan App din, Saika danna kan App din Daga nan Zai fara Downloading. 

Idan wannan Rubutu ya burge ku to kuyi Like akanshi sannan kuyi share domin 'yan uwa su amfana

Idan da wani gyara ko korafi to kuyi shi a comment, mungode.