1. Kada ka/ki bari yayi amfani da wayar "Android" don cire muku kudi

 Idan ka Æ™yale mai (POS) ya yi amfani da wayarsa ta Android don cire maka kudi, to za a adana bayanan katin ATM É—inka acikin wayar mutumin.  Wannan yana bawa Æ´an damfara damar amfani da bayanan katin ATM É—in ku don siyan kaya akan online.  Wasu masu POS za su ce maka babu Internet a machine dinsu, kuma za su yi amfani da wayoyinsu na Android wajen cire maka.  Idan babu Internet a machine dinsu na POS, karÉ“i katin ATM É—in ku ku tafi.

2. Kada ku bari ya shigar da lambar PIN na ATM din ku

 Wasu masu POS suna tambayar PIN na ATM na abokin cinikin su shigar masa da kansu. Ka tabbata ka saka PIN din ka dakanka lokacin da kuka je wajen me POS don cire kudi. Dalili kuwa shi ne wasu na’urorin POS an tsara su musamman don adana lambobin katin ATM, amma ba za su iya ajiye PIN É—in ba.  Babu wani dan damfara da zai iya cire kudi daga asusunku ba tare da samun PIN na ATM din ku ba.

3. Kada ku bari wani mai POS yayi ma  bankin ku Korafi a madadin ku

 Wakilin POS zai nemi bayanan katin ku don yin korafi ga bankin ku a madadin ku.  Zai aika bayanan bankin ku zuwa bankin ku akan Facebook, Twitter, ko Instagram.  Duk lokacin da masu kutse (Hackers) sukayi kutse a shafukansa na sada zumunta, wannan zaisa kudaden ku su zama cikin matsala.  Idan kuka sami matsala yayin amfani da na'urar POS don cire kudi, zan ba ku shawarar ku je banki da kanku don yin korafi.

4.Kada ka bar katin ATM dinka gurin wani Mai POS don cire maka kudi, koda kuwa ka san mutumin.

 Guraren POS ya kasance a kowane titi a yawancin sassan Najeriya.  Wannan ya sa kasuwancin yau da kullun ya kasance mai sauÆ™i don samun damar shiga saboda ba ya buÆ™atar ziyartar banki sau da yawa.  Duk da haka, na'urar POS ta zama kayan aiki da Masu damfara Suka zaba, waÉ—anda yanzu suka shiga cikin kasuwancin POS don samun bayanan katin ATM na abokan ciniki.

 Yayin da kuke ziyartar gurin mai POS don cire kudi, abubuwan da aka lissafa a sama wasu abubuwa ne da zaku iya yi don rage haÉ—arin hari akan kasuwancin ku ko asusun bankin ku. 

Idan wannan rubutu ya Burge ku to Kuyi like Sannan kuyi share domin 'yan uwa su amfana. 

-Wannan dai Domin samun tsaro ance kula da kayanka... 

Idan da wani gyara ko korafi to kuyi shi a comment dake Qasa

-Nasir Hassan Kankia