Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta bayyana cewa an samar da wata manhaja da matasa ke amfani da ita wajen yin sakamakon Bogi a jarabawarsu ta JAMB.

 Kuma suna fitar da sakamakon a cikin Jama’a domin jindadi da kuma karbar kudi daga hannun wadanda ba suji ba basu gani ba.

A cewar hukumar ta JAMB, wani Atung Gerald a Kaduna, wanda ya yi ikirarin cewa ya samu maki 380 a jarrabawar sa ta JAMB, an gano cewa damfara ce.

 A cewar hukumar ta JAMB, al’ummar Atung Gerald sun fito ne domin neman aba Atung Gerald matsayin da ya dace domin ya samu maki mafi girma a jarrabawar tasa ta JAMB.

Sai dai hukumar ta JAMB ta lura da cewa a lokacin da suka duba Na'urar su, sun gano cewa Atung Gerald bai ma yi rajistar jarabawar ta JAMB ba, don haka babu yadda za a yi ya samu maki 380 a jarrabawar da ba ya cikin ta.

Hukumar ta JAMB ta kuma bayyana cewa ba Atung Gerald ne kadai ke yin sakamakon Bogi a jarabawar JAMB ba a ‘yan kwanakin nan, domin hukumar ta JAMB ta gano wasu sakamakon na bogi da dama.

Daga Naku Har Kullum NHK 

Zaku iya Samun mu a Twitter NHKTECH, Facebook NHKTECH, da kuma Telegram NHKTECH. Sannan zaku iya Joining din WhatsApp group duk domin samun labaran mu Akai akai.