Diphtheria ƙwayar cuta ce wacce nau'in corynebacterium ke haifarwa, wanda cutar tana shafar hanci, makogwaro, a wani lokacin kuma, fatar mutum.

Wasu alamomin diphtheria sun haÉ—a da zazzabi, zubar majina a hanci, ciwon makogwaro, tari, jajayen idanu, kumburin wuya, da wahalar numfashi.

Da yake magana a wani taron manema labarai a ranar Litinin, Sadiq Abdulrahman, daraktan sashen kula da lafiyar jama’a na babban birnin tarayya Abuja, ya ce tuni cutar ta kashe wani yaro dan shekara hudu.

Abdulrahman ya ce an tabbatar da bullar cutar a babban birnin kasar bayan sakamakon É—aya daga cikin samfuran da aka dauka daga wadanda ake zargin sun kamu a wani kauye da ke kusa da yankin Dei-Dei.

Ya umurci mazauna yankin da su dauki tsafta da mahimmanci, kuma ya shawarce su da su kai rahoton duk wani bakon alamu, musamman, wanda ya shafi lafiyar numfashinsu ga hukumomin da abin ya shafa.

"Makonni biyu da suka gabata, mun sami bayanai daga wata al'umma a cikin Abuja, wanda hakan ya sa kungiyarmu ta dauki wasu samfurori," in ji shi.

"An kai samfurin zuwa dakin gwaje-gwaje na kasa, Gaduwa da NCDC, kuma daya daga cikin wadanda ake zargin ya kamu da cutar."

Daraktan ya ce sashen na hada kai da jihohin da ke makwabtaka da su domin tabbatar da ganin yadda cutar ke kara yaduwa ta hanyar sanya ido kan iyakoki.

Shima da yake nasa jawabin, babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko ta FCT, Yahaya Vatsa, ya ce mutanen da ba su yi wa allurar rigakafi ba, da wadanda ke zaune a cunkoson jama’a da rashin tsafta na cikin hadarin kamuwa da cutar.

Allah ya karemu daga dukkan bala'o'i da kuma Annoba.

Daga Naku Har Kullum NHK