Ad Code

Federal Government ta Kwato N58bn Daga Wadanda Take bi Bashi Mutum 7,000 – Cewar Director


 Gwamnatin Tarayya ta juya zuwa ga wadanda take bi bashi a ma’aikatu da hukumomi sama da 946 a fadin kasar nan, inda ya zuwa yanzu ta kwato N58bn daga gurin mutane 7,000 da take bi bashi.

 Daraktan Ma’aikatar Kudi, da Tsare-tsare na Kasa, Victor Omata, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wani taron wayar da kan jama’a kan shirin dawo da basussukan gwamnatin tarayya ta hanyar shirin Lighthouse a Asaba.

 Omata, wanda mataimakiyar darakta a ma’aikatar, Mrs Bridget Molokwu ta wakilta, ya bayyana cewa an kwato N58bn daga MDAs 11 zuwa yanzu.

 Ya ce, “Za ku tuna cewa daya daga cikin muhimman manufofin tattalin arziki na gwamnati mai ci, shi ne inganta kudaden shiga na gwamnatin tarayya ta hanyar kara kudaden shiga daga hanyoyin da ba na man fetur ba.

 “Manufofinmu da dabarunmu su ne yin amfani da fasahar bayanai na zamani don taimakawa wajen toshe hanyoyin samun kudaden shiga, gano sabbin hanyoyin samun kudaden shiga, inganta hanyoyin samun kudaden shiga, musamman kudaden shigar da ba na mai ba, da kuma ingantawa na kasafin kudi.

 “A wajen tabbatar da wannan buri, Ma’aikatar Kudi, Kasafin Kudi, da Tsare-tsare ta Tarayya ta kaddamar da ‘Shirin Lighthouse.

 “Bayanan da suka fito daga Shirin Lighthouse sun nuna cewa kamfanoni da daidaikun mutane da dama da akebi bashin sun ki biyan hukumomin gwamnati hakkokinsu.

 "A cikin N5.2tn, an kwato N58bn daga gurin wadanda akebi bashi 7,000 a cikin MDAs 11, kuma har yanzu aikin cigaba da amso basussukan yana cigaba."

Daga Naku Har Kullum NHK 

Post a Comment

0 Comments